Mutane masu fasaha da fikirar kirkira, musamman ma mawaka da ’yan wasan kwaikwayo na Hausa, a duk lokacin da suka furta wani abu, sukan haddasa nishadantarwa ko kuma fadakarwa. A ’yan kwanakin nan, mun tattauna da irin wadannan masu sana’a, kuma ga guda goma daga cikinsu, da kuma irin abubuwan da suka furta da bakunansu, a kan al’amura daban-daban.
(1)-Umar Nagudu, mawakin Hausa na zamani. An tambaye shi cewa: To, ko za ka gaya mana abin da ya ba ka sha’awa har ka shiga sana’ar wakar Hausa? Ya amsa da cewa:
“Abin da ya ja hankalina har na ga cewa ya kamata in shiga harkar waka shi ne, idan ina sauraren wakokin wasu mawakan, nakan yi la’akari da irin sakonnin da suke aikawa ga al’umma, wanda haka ya sanya har ma mutane kan zama sun fadakantu daga darussan wadannan wakoki. Wannan ne ya ban sha’awa kuma na ga cewa ni ma ya dace in shiga cikin harkar domin in ba da tawa gudunmowa ga al’umma.”
(2)-Haruna danjuma (Mutuwa Dole). An tambaye shi cewa: Yaushe ne ka fara wasan kwaikwayo? Ya amsa da cewa:
“Na fara wasan kwaikwayo tun ina makarantar firamare, ina dan shekara 11. Na shiga firamare ina dan shekara 7, na shekara 4 ina aji hudu, muka fara wasan kwaikwayo. Tun muna yi tsakaninmu yara har ya zamanto muna yi a gidan masaukin baki, domin a lokacin mulkin En-e En-e, muna zuwa gidan muna yin wasannin; inda yara kan biya ’yan kudi su kalla. Har daga nan na samu hikimar yanke hotunan Kaboyi, ina yin silima nawa a gida, ina samun katon na suga da fitilar A-ci-bal-bal, yara na biyan kudi suna kallo, a zauren gidanmu.”
(3)-Hussaini BBC. An tambaye shi cewa: Baya ga daukar hoto, na kuma ji cewa kai mawaki ne, to yaya ka shiga harkar waka? Ya amsa da cewa:
“Gaskiya fisabilillahi, ina yin harkar waka, sai dai na fi karfi a wakokin yabon manzon Allah. Amma yanzu ina yin ta siyasa, don an fi sanina a harkar wakar siyasa. Na shiga harkar wakar siyasa don in fadakar da talakawa da al’umma, kan cewa su rika zabar abin da zai fitar da su daga cikin kunci, ba wai masu yi musu karyar zan yi kaza, zan yi kaza ba.”
(4)-dan Auta (Mai wasan barkwanci). An tambaye shi cewa: Akasarin wasanninka, kana nuna wauta a ciki. Ko me ya sa kake yin irin wannan fita tare da jero maganganu wasu na bin wasu, to rubutawa kake yi ne ko yaya kake yi? Shi kuma ya amsa da cewa:
“Wasan kwaikwayo da ban dariya ko wauta, na sanya mutane sha’awar kallon abin da ake yi, su kuma dauki darasi daga ciki. Kuma abu ne daga Allah, ba na rubuta komai. Ina fadi ne kurum a jere har mutane su gamsu. Kuma ina yin wannan wasa ne a ko’ina aka gayyace ni.”
(5)-Hamisu Lamido Iyan-Tama (Mai shirya fina-finai kuma dan wasan Hausa). An tambaye shi cewa: Ko akwai wani abu takamaimai da ya faru a tsakaninku da Biba Problem, kamar magana ko wani al’amari, wanda za ka iya tuna ta da shi da zarar an ambaci sunanta? Ya amsa da cewa:
“Marigayiya Hauwa Ali Dodo, akwai wani abu da ya faru tsakanina da ita, wanda nakan tuna ta sosai a kansa. Wannan al’amari kuwa shi ne, a duk lokacin da muka hadu da ita, takan kira ni da wani suna, ni ma nakan kira ta da wani suna. A duk lokacin da muka hadu, sai ta fara kira na da wannan suna, sannan ni ma in kira ta da nata sunan, sannan mu fara magana. Watau a duk lokacin da muka hadu, za ka ji ta kira ni da cewa: “Zagadada!” Ni kuwa sai in ce mata: “Haba Hauwa’u? Ai tun da kin auri mai arziki sai ki rike kudin ni kuma in tafi…” Da zarar mun fadi haka ga juna, sai ta kyalkyace da dariya. Wannan al’amari, ba na mantawa da shi a duk lokacin da batun Hauwa Ali Dodo ya fado mani a rai.”
(6)-Carmen McCain (Talatu Baturiya). An tambaye ta cewa: Ko za ki yi mana bayanin yadda aka yi ma kika samu kanki wajen sha’awar magana da harshen Hausa, wanda a yanzu kin zama babbar daliba da ke koyo da nazartar harshen? Ta amsa da cewa:
“Idan kana nufin yadda ma na fara koyon harshen Hausa ne, sai in ce maka ni na girma ne a garin Jos, domin kuwa babana Farfesa ne a Jami’ar Jos. Lokacin da nake zaune da iyayen nawa a Jos ne na fara dan koyon magana da harshen. Na fara da koyon gaisuwa, irin kamar ‘Sannu, ina kwana?’ da dai irin wadannan maganganu da ake yi na yau da kullum, musamman ma idan na je kasuwa. Amma lokacin da na koma Amurka, na fara karatun digiri na biyu a Jami’ar Wisconsin, sai suka ce mani ya zama dole in dauki wani kwas na musamman kan nazarain harsunan Afrika,. Dalili ke nan na tuna da cewa, ina iya magana kadan-kadan da harshen Hausa, don haka zan ci gaba da nazarin harshen ma gaba daya. Tun daga nan na fara halartar kwasa-kwasan Hausa a nan jami’ar, inda daga bisani da na zo Najeriya, sai na je Sakkwato, inda na ci gaba da koyon harshen na Hausa. Amma a lokacin, malamina, Dokta Malami Buba, a lokacin nan yana Jami’ar Usman danfodiyo, shi ne ya kawo mani fina-finai da littattafan Hausa, na fara karanta littattafan da kuma kallon fina-finan, wannan shi ya kara ba ni sha’awa da kwarin gwiwar son harshen, domin a da, ina nazarin harshen ne saboda dokar da aka ba ni a jami’a ne kawai, ina tunanin zan yi rubutu kan littattafan Najeriya, amma da Turanci, sai dai na san zan dawo Najeriya domin in yi amfani da shi, amma ba na tunanin zan yi amfani da shi a bincike na. Amma lokacin da na fara kallon fina-finan Hausa, kuma na fara karanta littattafan Hausa, sai na ce dole ne ma in fara bincike a kansa, domin kuwa akwai mutane da yawa a waje, wadanda ba su san ma cewa akwai ayyukan fasaha na Hausa ba. Haka kuma, wasu na cewa babu bunkasuwar karance-karance a kasar Hausa, ni kuwa sai na ga ba haka ba ne, domin na ga cewa akwai mutane da yawa da ke kallon fina-finan Hausa kuma suke da sha’awar littattafan Hausa, dalili ke nan ya sanya na ga ya kamata in yi nazari a wannan fanni.”
(7)-Shehu Ajilo danguzuri. An tambaye shi cewa: An ce kana da alaka da marigayi Dokta Mamman Shata Katsina, ko za ka yi mana bayani game da dangantakarka da shi? Ya amsa da cewa:
“Muna da alaka da Shata, musamman don kauna, ina daya daga masu kaunar kalmominsa da abubuwan da yake fadi. Akwai lokacin da makada da mawaka da maroka suka hada wata kungiya, musamman saboda adawa da gaba da Shata. Da farko ina tare da su, har zuwa lokacin da aka je wani taro Kaduna, aka ce za a ba ni Sakatare. Na ce ba ni so, aka ce za a ba ni Ma’aji, na ce ba ni so, aka ce za a ba ni shugabanci, na ce ba ni so. Bisa ga haka wani cikinsu ya kebe ni, ya ce me ya sa ba ni son mukami a kungiyar? Na ce saboda na ga cewa ba don Allah aka kafa kungiyar ba, an kafa ta ne saboda a yi gaba kuma a musguna wa wani mutum daya kuma duk inda ka ce sai ka ci mutuncin wani, to ka jira Allah; koda Kafiri ne kuwa, bare Shatan nan Allah Ya riga Ya nuna shi ga jama’a, a duniya fiye da mu. Idan mun kai mu dubu, da an ce ga Shata, karyarmu ta kare. Dalili ke nan ya sa na kauce wa wannan kungiya. Ina nan haka, sai jarida ta fita da labarin. Da aka karanta wa Shata cewa ga abin da Ajilo ya fadi, wannan shi ne sanadin da na auri diyarsa. Marigayi Shata ya kira ni, ya ce zai ba ni Maji Dadin Shata, na ce ba ni son wannan mukamin ranka ya dade, domin rawanina a gidanka daga Allah yake. Wasu mawaka kan nemi zolaya ta, ni kuwa sai in ce masu, duk cikin mawakan Najeriya, wa ya auri diyar Shata idan ba ni ba? Don haka ni a gidan Shata Yarima ne ni, dan sarki ne ni. Wannan ita ce alakata da shi, akwai kauna tsakaninmu.”
(8)-Alkarina Ahmad Muhammad. An tambaye ta cewa: Kin ce iyayenki sun ki yarda ki shiga harkar fim, to yaya aka yi yanzu kika samu kanki cikin harkar? Ta amsa da cewa:
“Kamar yadda na gaya maka, lokacin da na shaida wa iyayena bukatata ta shiga sana’ar fim kuma suka ki yarda, na bi ra’ayinsu, sai ban shiga ba. Ni kuma ga shi ban koma makaranta ba domin ci gaba da karatuna. Bisa ga haka, akwai wani yayana, wanda ya nace yana ba ni shawarar cewa lallai ya kamata in koma makaranta. Wannan ta sanya na amince da shi, na koma makaranta. Na tafi Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Hassan Usman Katsina, inda na fara karatun Diploma kan aikin jarida. Bayan na fara karatun nan, sai na tafi Kano, na hadu da wani mutum mai suna Bashir, na nuna masa cewa ina son shiga harkar fim, watau ba tare da iyayena sun sani ba. A lokacin da na shaida masa haka, sai ya ce mani babu wani abu, domin kuwa harkar fim tasu ce, domin a daidai lokacin ma suna cikjin aikin shirya wani fim ne. Shi ne ma ya ce mani, idan zan iya zuwa, za mu tafi wajen da ake shirya fim din, domin in ga yadda ake yin komai. A lokacin sai na amince, muka tafi garin Gumel, inda Sa’idu Gwanja ke shirya wani fim dinsa, na kalli yadda ake shirya wannan fim, har ma a lokacin nan aka sanya ni na fito cikin fim din, har ma gurbin da aka ba ni da akwai waka.”
(9)-Sagolo (Mawakin Maza). An tambaye shi cewa: A cikin tsawon shekarun da ka yi kana kidan kokowa, wace kokowa ce ta fi ba ka sha’awa, sannan wacce ce ta fi ba ka al’ajabi? Ya amsa da cewa:
“In dai a kada mutum ne, to kayin kokowa nufin Allah ne. Ka san kura da ta taka kwado sai ta ce sa’ar kafa; ba don shi ta fito ba, amma kuma ba za ta bar shi ba. Ka san kayin da Laminu Mai Dabba ya yi bara, wanda ya ci takobi, sa’ar kafa ce, domin bai yi tsammanin zai yi kayi ba amma sai Allah Ya ba shi sa’a. Haka kuma sanda wata ’yar shamuwa ta Jihar Difa, watau Kari Bulaye, ya kada Kadade, wanda shi ma bai yi tsammanin zai yi kayi ba, amma sai ga shi ya yi. Saboda haka, abin daga Allah yake. In da mutum ne yake ba da takobi, to tun da aka fara kokowar takobi da Kadade zan bai wa. Don bai da kashe ni ka diba, amma yanzu kana ganin ’yan kokowa kowa lake da aljihunsa kusa da jikinsu. Wadannan ya zan iya samun kudi daga wajensu. Amma shi Kadade, in ya samu kudi ni yake bai wa. Kuma har ya ce mini in tafi gidansu in yi roko. Da na je, dabba goma sha bakwai ya ba ni, akuya shida da tunkiya biyar da shanu biyar da rakumi da kudi jaka maitan da santolo shida da hatsi. Ai Adarawa ba su haifi da kamar Kadade ba.”
(10)-Sani dan Indo. An tambaye shi cewa: Idan muka dawo kan ita wannan sana’a ta waka, me ya ba ka sha’awa kuma ya ja ra’ayinka har ka zabi ka zama mawaki? Ya amsa da cewa:
“Wannan sana’a ta waka dai ba gadonta na yi ba, abin da na gada ita ce sana’ar Fawa. Gidanmu na daya daga cikin masu sarautar Fawa a Gusau. Kamar yadda na fara gaya maka da farko, ina dan shekara bakwai, a lokacin nan ina tallar tsire. Duk lokacin da Sani Kaka Dawa ya zo da jama’arsa yana wasa, sai kawai in ji a raina cewa wannan tallar tsire ba ta yi mini ba, sai na ji kawai ina sha’awar sana’ar nan da Sani Kaka Dawa yake yi, watau kida da waka. Tun ina zuwa kallon wasan nasu, har na yanke hukuncin shiga sana’ar. Lokacin da na fara bin su kuwa, ba su wulakanta ni ba. Haka na fara tafiya tare da su har iya lokacin da na fara cin gashin kaina. Na samu kimanin shekara tara tare da Sani Kaka Dawa, ban iya waka ba, sai dai in yi masa kida da kuma amshi.”