Sunday 13 February 2011

ADAM A ZANGO



  • BA kamar Zangon Daura ko Unguwar Zango Bare-Bari da ke cikin Jihar Kano ba, wa]anda wurare ne da suka yi suna a tarGhin }asar Hausa, Zango Kataf gari ne wanda yawancin mazaunan sa }abilar Katafawa ne. garin ya yi }aurin suna kuma ya ajiye mummunan tarihin fa]an }abilanci da na addini inda aka kashe ]aruruwan mutane. A wannan garin ne aka haifi Adamu Abdullahi, ko kuma mu ce Adam A. Zango, fitaccen jarumin nan da aka sani da la}abin ‘Usher’.


    A lokacin da aka yi rikicin Zango }ataf, Adam yana yaro }arami inda yake karatu a makarantar ‘Zango 1 Primary School.’ A hirar da ya yi da wakilinmu, jarumin ya labarta mana cewa, "Lokacin da rikicin kashe-kashen Zango Kataf ya ~arke, ni ina }arami, kusan ban san komai ba. Sai ma ~oye ni da aka yi kamar yadda aka ri}a ~oye sauran yara }anana".


    A nan sai Adam ya sunkuyar da kai ya tuna abin da ya gani a lokacin rikicin. "Ka san bayan an yi kwanaki ana rikici, to daga bisani ‘yan sanda sun zo suka tcsirar da mu daga harin {atafawa. To a gafen titi na ga tulin gawarwaki birjik, har da na wa]anda na sani."


    Ba wannan bala’in ka]ai Adam ya gani ba. Ya }ara da cewa ya ga yadda aka ri}a banka wa gidaje wuta suna }onewa }urmus.


    Adam ya }ara da cewa daga nan ne wani kawunsa mai suna Alhaji Rabo Musa Salisu ya ]auke shi tare da sauran dangi ya ranga]a da su garin Jos. Ko Adam ya san gwarzon Katafawa wanda aka yi wa shari’a bisa zargin shi ne ummulhaba’isan kisan kiyashin da aka yi, wato Janar Zamani Lekwot, ido da ido kuwa? "A’a, ni ban san shi ba, sai dai sunansa da kuma aika-aikar da ya aikata kawai na ke ji, inji Adam.


    Adam bai da]e a garin Jos ba sai kawunsa ya sa shi makaranta. A Turance, ya ce mana, "I was enrolled in Islamiyya primary school. When I finished, I was later admitted at Government Secondary School, Laranto." wato yana nufin ya yi karatun Islamiyya, da ya gama aka saka shi a makarantar Sakandaren Gwamnati ta Laranto.. Kun san a industiri akwai magulmata masu cewa wai Adam Bakatafe ne, ya saje da Hausawa yana yin fim. Har ma wasu na cewa ba su san ma’anar ‘A’ ]in nan ta tsakanin sunansa ba.


    Da aka yi masa tambaya kan ha}i}anin gaskiyar salsalar sa, sai Adam ya gyara zama ya ce, "To yau dai tun da an tambaye ni, bari in fa]a ga duk wanda ya damu ya sani ko ya ji. Ni dai Bahaushe ne cikakke, ba Bakatafe ba."


    Ya ci gaba da cewa, "Da farko, kakana zuwa Zangon Kataf ya yi, daga shi kuma mahaifina ya ha]u da mahaifiya ta ne a Saminaka, suka yi aure, suka dawo Zangon Kataf da zama, inda aka haife ni."


    Adam ya }ara bin tushensa inda ya ala}anta kansa da jinin Larabawan Shuwa. "Kai, ni fa akwai jinin Shuwa Arab a jiki na, domin mahiifiya ta tana da jinin Shuwa Arab ajikinta".


    A halin yanzu Adam ya dawo da mahaifiyarsa Kano inda ita ma take ]an]ana romon ribar industiri. "Ni ban ga dalilin da zai sa in bar mahaifiya ta can nesa ba, na fi so in matso da ita kusa da ni. Kuma na gode Allah da azurtawar da a yi min. don haka wajibi na ne in kyautata wa mahaifiya ta."


    To mu ci gaba. Da yake Adam (komu ce Adamu) bai yi nufin ci gaba da karatu ba, yana kammala karatun sakandare a Laranto, sai ya tarkato kayansa ya nufo Kano, kaitsaye ya zarce gidan buga wa}o in fina-finai na ‘Lenscope Media’ mallakar furodusa/darakta Sani Mu’azu, wanda shi ma ]an Jos ne.


    "Shekara biyu na yi ina cin ba}ar wahala a ‘Lenscope Media’ inji Adam. "Haka nake zaune ina kallon kaina a matsayin jarumi, amma har zuci na san ni ba jarumin ba ne, saboda idan na yi sin ]aya, ban san ranar sake yin wani ba."


    Yana cikin irin wannan zama ne sai sakatariyar kamfanin Lenscope ]in, mai suna Hauwa M.D. (Kun tuna ta?) Ta fara tausaya masa ganin cewa matashin ]an fim ]in yana cikin halin rayuwar na ware-ga-dangi. Sai ta ba shi shawarar me zai hana ya koyi yadda ake ki]a, wato buga wa}a.


    Da farko Adam bai ]auki shawarar ba, sai ya nuna mata cewa, "Ni fa na zo Kano ne don in zama jarumi in yi fim, ba in buga wa}a ba."


    Amma da ya ga uwar bari, kullum mafarkin zaman sa jarumi na }ara faskara, sai ya nemi fitaccen maka]in nan Ibrahim Danko ya ri}a koya masa yadda ake buga wa}ar a Lenscope ]in. "Gaskiyar magana ka ji yadda aka yi na zama maka]i ba a son raina ba."


    Cikin }an}anen lokaci aka san Adam A. Zango a matsayin maka]i, domin ya buga wa}o}in fina-finai masu yawan gaske.


    Shin ya ya aka yi bayan ya zama mashahurin maka]i kuma ya riki]e ya zama fitaccen jarumi?


    Ya ba mu labarin: "To da na tara ku]in da zan iya yin fim, sai na yi tunanin in yi fim nawa kuma in zama jarumin fim ]in nawa tunda matsayin jarumi."


    Da wannan ne ya yi fim ]in sa na farko a matsayin jarumi mai suna ‘Surfani.’


    Adam ya yi suna a fina-finan soyayya, musamman fim ]in sa ‘Raga, wanda a yanzu ake kiran sa da suna fim ]in, wato Mai Raga. Amma ‘Zabari,’ Kallabi’ da irin su ‘Kawanya’ ne suka fara fito da shi. Wannan tashe da ya yi kuwa ya sa Adam ya yi wa matasa masu buga rol na soyayya zarra. Ko a gida ko a lokeshin ko a fim, inda Adam yake za a gan shi ‘yan kallo suna baibaye shi. Ofishinsa na buga wa}a mai suna ‘Crown Studio’ kuwa wata matattara ce ta matasa maza da mata. Sai dai kuma duk da wannan, shi Adam muradinsa tun farko shi ne ya zama wani tantirin ma}etaci, ]an daba, bos, irin su Shu’aibu Kumurci.


    To ya ya aka yi ya zama jarumin soyayya?


    Ya ce, "Gaskiya Ali Nuhu ne zan iya ce malamina. Shi ya koya min yadda ake yin rol na soyayya. Kai, sai da ta kai Ali kan zaunar da ni yana koya min yadda zan ri}a yin kukan jimamin soyayya a fim. To yanzu ga shi ina jin da]in wannan rol ]in, don ya kar~e ni."


    Shin Adam yana sane da yadda ‘yan mata ke yi masa son daga-nesa-nesa kuma masu yawan bugo masa waya fa?


    Sai ya amsa da cewa, "Ai ina sane, mahaifiyata ce ke ce min in ri}a yin kaffa-kaffa da ‘yan matan zamani. Shi ya sa ma take ta bi na da lallami cewa in yi aure kawai ko sa shafa min lafiya."


    To Adam A. Zango muna jiran mu ga wannan rana ta aurenka. Haka su ma ‘yan matan naka, suna jira

3 comments:

  1. Hmm ni maisan wasankane asanadiyyanka nayi mussuda wani jiniyor awurin aiki SBD no fans dinkane

    ReplyDelete