Sunday 13 February 2011

Misbahu M. Ahmad

Fitaccen mawakin Hausa na zamani kuma dan wasan fina-finan Hausa, Misbahu M. Ahmad ya auri fitacciyar ’yar wasa, Maryam Aliyu Umar. An daura auren ne a ranar Juma’a da ta gabata, da misalin karfe goma na safe, a unguwar Gwammaja, kusa da gidansu ango Misbahu, a cikin birnin Kanon Dabo.
Auren da aka daura shi a kan sadakin Naira dubu hamsin, wanda kuma aka biya lakadan ba ajalan ba, ya dauki hankalin mutane sosai, musamman ma ganin cewa wannan ba shi ne auren angon da amaryar na farko ba. Ita dai amarya Maryam, wacce kyakkyawa ce, ’yar asalin kasar Nijar, daga kabilar Bugaje, ta taba auren fitaccen dan wasa Shu’aibu Lawan, wanda aka fi sani da lakanin Kumurci a fina-finan Hausa. Kodayake auren bai yi tsawon kwana ba, ya mutu shekaru biyu da suka gabata.
Shi kuwa angon nata, Misbahu Ahmad, wanda fitaccen mawakin zamani ne na Hausa, ya taba yin aure kodayake ba ’yar fim ba ce ya aure. Kafin auren nasa na farko, ya yi kokarin auren fitattar ’yar wasa, Rukayayya Umar Santa, wacce aka fi sani da lakanin Dawayya, amma haka ba ta samu ba, duk da cewa suna kaunar juna sosai.
Fitattu daga cikin ’yan wasan fim da suka halarci daurin auren, sun hada da fitaccen mawaki, Aminu ALA da mawaki Mudassir Kassim da Ibrahim Mandawari da Abdulhadi (Awilo). Sauran sun hada da Baba karami da sauransu da dama da suka halarci auren.
Kafin ranar daurin auren, a ranar Laraba, 16 ga wannan watan, tawagar anguna da ta amare, sun tattaru a otel din Alliance France da ke birnin Kano, da dare, inda suka gudanar da kwarya-kwaryan biki. ’Yan wasa da suka samu halartar bikin kuma suka taka rawa sun hada da Rashida Adamu Abdullahi da Abubakar Baballe Hayatu da Hauwa Ali Dodo, wacce aka fi sani da lakanin Biba Problem da kuma Daso. Sauran sun hada da Lubabatu Madaki da Tahir I. Tahir da mawaki Adamu Nagudu da Umar Gombe da Fauziyya Mai Kyau da Maimuna HRB da Salisu Gombe, da sauransu.
A wurin shagalin, an gabatar da kade-kade da raye-raye, sannan kuma maza da mata sun yi kwalliya da shigar Buzaye, kasancewar amaryar ’yar kabilar Bugaje ce.

4 comments: