Sunday 13 February 2011

YADDA ZAKARUBUTA LABARIN FILM

A nan, ana so marubuci ya bayyana labarin tun daga labari a takaice, fadada labarin har zuwa wajajen (locations) da za a dauki shirin fim din.Wanda a nan ne marubuci zai bayyana halaye da dabi’un wadanda suke fim din (characters), zai kuma rubuta zantuka (dialogues) da za a yi a fim din, zai kuma rubuta wajajen da za a dauki shirin fim din.
Misali, cikin kayataccen lambu mai yawan furanni da dogayen bishiyoyi, Amin ne da A’isha suke gudanar da hirarsu ta soyayya, ana saura kwanaki uku bikinsu.
“Amarya, kin sha kamshi; amarya ba kya laifi ko da kuwa kin kashe dan masu gida.” Ya fara da zolayarta.
Dariya kawai ta yi, don ta san shi gwani ne wajen zolaya.
“Ango ka sha kamshi, ango ba da kanka a sare, ka je gida ka ce ya fadi.” Ta ce da shi bayan ’yar karamar dariyar da ta yi.
A nan marubucin ya fitar da wajen da za a dauki shirin fim din, ya kuma sanya zantukan da za a yi a wajen daukar fitowar (Scene).
Misalin halayya kuma ga su kamar haka:
Ibrahim, shiru-shiru, mai yawan fara’a. Amina, marar kunya da rashin mutunci. Karime, ballagaza marar kamun kai. Alhaji Idi, mai zafin rai, wanda ba ya so a raina shi da sauransu.
Haka a wannan rukunin ake so marubucin fim ya fitar da abubuwa kamar haka:
Lokacin daukar shirin fim (Shooting Time). Misali, safe, rana, dare, yamma da sauransu.
(i)-Wajen daukar shirin fim, wannan ya kasu kashi biyu; a ciki (Interior) da kuma a waje (Edterior). Misali, a ciki, akwai daki, falo, cikin mota da makamantansu. Misalin a waje, akwai kan titi, a daji, a farfajiyar wani waje, da sauransu. Don haka ne ake son marubuci ya tantance inda za a yi daukar shirin fim.
(ii)-Tsarin daukar hoto (Scene List or Scene Number).
A nan, ana so marubucin fim ya fitar ko ya tsara yadda za a dauki fim, wanda zai bayar da lambar daukar hoto ne ga kowace fitowa (Scene Number).
(4)-Tsarin yadda za a dauki labarin fim da kyamara (Shooting Script).
A nan, marubuci zai rubuta tsarin yadda za a dauki shirin fim ne, ta hanyar yin amfani da zirga-zirgar kyamara ta bangaren:
(4a)-Kusurwar Hange (Angle of biew).
Ana so marubuci ya rubuta kusurwar hangen da yake so kyamara ta kasance tsakaninta da abin da ake dauka (Subjet) ko inda aikatau (Action) ke faruwa. Misali, kasa-kasa ne (Low Angle); daga sama ne (High Angle) ko kuma saitin ido (Eye-Lebel Angle) ko zuwa rabin jiki (Portrait), ko kuma gaba daya surar mutum ko gaba daya inda aikatau ke faruwa (Complete Subject or Action).
(4b)-Fagen Hange (Field of biew).
A nan, ana so marubuci ya bayyanar da nisan ko tazarar da ke tsakanin kyamara da abin da take dauka (Subject), ko kuma inda aikatau ke faruwa (Action). A nan ake bayyana cewa daukar kusa-da-kusa ne (Close Shot), ko daukar nesa (Long Shot), ko kuma matsakaicin dauka ne (Medium Shot), ko juya kyamara za a yi (Upside Down).
(4c)-Zirga-zirgar kyamara (Camera Mobement).
Ana so marubucin fim ya zayyana yadda kyamarar za ta rika zuwa da komayya ga abin da take dauka (Subject), ko inda aikatau ke faruwa (Action). Idan mutum ya kalli saman daki ko sararin samaniya ko dai wani abu da ya fi mutum tsayi, ko za a daga kyamara zuwa kallon sama, to marubucin zai bayyana cewa kyamara za ta gyada kai (Tilting). Haka idan mutane suna da yawa kuma ana daukar su a shirin fim, idan suna magana, a nan kyamara yawanci waige-waige take, saboda lokacin da suke magana kyamarar za ta rika daukar mai magana; shi ya sa ake so marubucin ya bayyana duk irin waige (Pan) da kyamara za ta yi yayin daukar shirin fim. Ko kuma kyamarar za ta zauna a kurar daukar hoto ne (Dolly).
(4d). Yanayin sadarwa don bambamcewa daga dauka zuwa dauka, ko daga fitowa zuwa fitowa. A nan, marubuci kan rubuta ko tsara yadda yake son hakan ya gudanu. A cikin yanayin sadarwa akwai hoton da zai dinga daukewa ne kamar daiman (Diamond), dusashewa (Fading), narkewa (Dissolbing), rugujewa (Shattering), wannan ya kasu kashi da yawa. Wani kan yi dama (Right), hagu (Left), sama (Up), ko kasa (Down). Wani nau’in sadarwar tsakanin dauka da dauka kan zo da tafiyar tsutsa (Zig-Zag), wanda ya kasu kashi biyu, a kwance (Horizontal) ko a tsaye (bertical) da sauransu.
Sanin ka’idojin rubutu kafin rubuta labarin fim
Yana da kyau, ya kuma zama wajibi marubucin labarin fim ya san ka’idojin rubutu, wanda ta haka ne kawai za a iya fitar da ma’anonin zantuka a cikin labarin fim.
Misali, Musa ya tafi gida. Musa ya tafi gida? Ka ga jimla ta farko ta nuna cewa Musa ya riga ya tafi gida (Statement). Amma jimla ta biyu, tambaya take shin ko Musa ya tafi gida? Ka ga ke nan, idan marubuci bai san ka’idojin rubutu ba, to zai matukar ba wa ’yan wasa ciwon kai, kuma shirin zai samu nakasu. ka’idojin rubutu da suka kamata marubucin fim ya sani sun hada da Aya (.) (Fullstop), Wakafi (Comma) (,), Alamar motsin rai (!) (Edclamation Mark), Alamar tambaya (kuestion Mark) (?), Ruwa Biyu (Colon) (:), Baka Biyu {( )}, Alamar zancen wani (‘ ’ ko “ “), Sanda-Jirge (/) da sauransu.
Ta hanyar wadannan ka’idojin rubutu ne kawai, labarin fim zai fita sumul, ba tare da Doma-Dol ko kuskure ba.

4 comments:

  1. muna godiya sosai Allah ya Ζ™ara basira.

    ReplyDelete
  2. Enter your comment... Allah yasaka

    ReplyDelete
  3. Munji dadi sosai da wannan bayanan yanxu haka inada rubutattun fina finai masu yawa ya zanyi in saida wadannan labaru da na rubuta

    ReplyDelete